Wadanda ake zargi sun musanta laifin yayin da aka karanta masu laifufukan su a gaban alkalin.

Wata kotun shari’ar musulunci dake gudanar da zamanta a garin Gusau ta tura shugaban karamar Hukumar Gusau Hon. Ibrahim Tanko gidan yari.

A Rahoton da jaridar Rariya ta fitar, zai ziyarci gidan kaso  tare da kansilan hukumar mai wakiltar mazabar sabon gari Hon. Ashiru Musa Nagari tare da shugaban jam’iyar APC na mazabar sabon garin Gusau Mainasara Yahaya.

A zaman da kotu tayi an zargi su da sa hannun wajen jefa al’kurani mai girma a bandaki.

Wadanda ake zargi sun musanta laifin yayin da aka karanta masu laifufukan su a gaban alkalin.

Mai shari’ar Muhammad ST, Shinkafi ya bada damar a cigaba da rikon su a gidan kaso har sai bayan kotu ta nemi  shawarar gwamnatin jihar Zamfara kan laifin su.

An daga ranar saurarar hukunci zuwa 26 ga watan febreru 2018.

 


Source: Pulse. Ng