Ganduje ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 44 dake jihar Kano

Alkalin alkalai na jihar justice Ibrahim Mukhtar ya rantsar da su a bikin wanda aka gudanar a wajen taro dake filin Sani Abacha stadium.

Gwamnan jihar Kano Alhaji Umar Ganduje ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomia daren jiya lahadi 12 ga wata 2018.

Hukumar zabe na jihar Kano ta gudanar da zaben kananan hukumomi ranar 10 ga wata wanda jam’iyar APC ta lashe a ko wani karamar hukuma.

Shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484 aka rantsar.

Alkalin alkalai na jihar justice Ibrahim Mukhtar ya rantsar da su a bikin wanda aka gudanar a dakin taro dake filin Sani Abacha stadium.

 

A jawabin sa bayan rantsuwar, gwamna Ganduje ya gargadi sabbin shugabannin da su zama jagororin yankunan su kuma su kasance masu aikin cikin adalci da tsari.

Gwamnan yayi kira ga sabbin shugabannin da su kwatanta irin ayyukan cigaba da gwamnatin jihar take kuma su kasance jakadun samad da ayyukan cigaba tun daga ko wani shiyya na kananan hukumomin su.

Daga karshe gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar zata hada gwiwa da  kananan hukumomin wajen samad da cigaba.


Source: Pulse. Ng